A ci gaba da samun abubuwan al’ajabi ko wani kaulin a kira shi da almara, Wata Matashiya mai karatun likita a Najeriya mai suna Dorcas ta bayyana yadda saurayin ta ya yaudare ta bayan ya sanya ta bar karatun likitan nata.
Matashiyar ta ce saurayin nata ne ya shawarce ta da ta bar karatun na likitanci ta koma farnin Shari’a saboda samun sa’ida, kuma nan da nan ta amince da bukatarsa saboda tana matuƙar kaunarsa.
Ta ce sun yanke shawarar hakan ne don kare shi a gaban kuliya duk lokacin da wata Shari’a tashi ta taso izuwa kotu.
Cikin sakon da ta wallafa a shafin sada zumunta na TikTok, Dorcas ta ce saurayin nata shahararren mawaki ne, wanda kuma komai ka iya rinchaɓewa, don haka ne suka nemi wannan mafita da zarar wata balahira ta kai shi gaban kuliya da ake kira manta sabo.
Sai dai ta ce kwanaki kadan bayan wannan mataki ne saurayin nata ya sanar mata da cewa fa ba shi ba ita, kowa ya kama gabansa.
Yanzu haka matashiyar ta ce rayuwa ta yi mata ɗaci ta inda babu yadda za ta sa kanta, har take ji tamkar ta bar duniyar nan.