Wani matashi mai shekara goma sha tara mai suna Ibrahim Kabiru yana tara Naira dubu daya da dari biyar ko wace rana, yayin da a wata Jimilla yana tara naira dubu arba’in da biyar a sana’ar yankar farce.
Kabiru Ibrahim wanda ke sana’ar tasa a birnin Benin ya shaida wa Kamfanin dillancin labarai na Kasa NAN cewa sana’ar tana rufa masa asiri matuka.
Ya ce ya tashi ne takanas ta Kano daga Jihar Sokoto don gudanar da sana’ar neman na sawa a bakin Salati.
Ko da yake a cewar yana matukar jigata irin yadda yake zirga-zirgar kewaye fadin kwaryar Benin, to amma fa lallai yana matukar alfahari da sana’ar kasancewar bai zama mai dogon hannu ba.
A cewar shi a baya yana sha’awar noman masara, amma sakamakon rashin kudi haka ala tilas ya jingine nomar ya rungumi sana’ar yankar farce.
Ya kara da cewa duk irin wadannan kudade rababa da yake samu, amma idan ya samu tallafin noma zai koma ya rungumi sana’ar ta duke tsohon ciniki.