
- Ina samun dubu 400,000 a duk wata, WANI Matashi Mai sayarwa barayi biredi
- Jami’an tsaro sun cafke wasu matasa dake kaima Yan bindiga biredi a wajejen Damari, Kidandan da Kuma Awala har zuwa Galadimawa dake karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna.
Jaridar Vanguard ta tattaro labarin aukuwar lamarin wajan Mai jagorantar jami’an tsaro Abba Kyari, Wanda ya Sami labaran tun takwas ga watan juni wajan wani kwararren Mai baima Yan bindiga labari dake yankin Zariya.
KARANTA:-Sojojin sun kwato shanu kimanin 155 da Rago da Rakumi a jihar Zamfara
A lokacin da ake zantawa da wadanda aka kama sunce “suna kaima Yan bindiga biredi ne a kauyukan Galadimawa, Damari, Awala da Kuma Kidandan.
Hassan Magaji Mai kimanin shekaru 29, yace ” shi Dan garin Galadimawa ne Yana da mata biyu da yara uku”. Yace “ya fara sana’ar biredi ne tun shekarar 2018″
Haka Kuma abokin aikinsa Auwal Abubakar Mai kimanin shekaru 24 yace ” nasan da cewa masu sayan biredi a gurinmu Yan bindiga”
Ya cigaba da cewa ” Yana da mata da Diya guda daya nayi makarantar Allo Kuma dama shi manomi ne iyaka ya shuka ya jira idan lokacin yayi sai ya gyara.
Yace ” amma kamin lokacin nakan Dan Sami wani aikin da zanyi” yace na fara aiki ne da Magaji tun wata uku da suka wuce.
Cikon na ukunsu Shima Mai kimanin shekaru 17 Wanda ake kiransa Ibrahim yace ” ya fara karantun Firamare amma ya gudu yace Shima Dan garin Galadimawa ne.”
Yake cewa “Yan bindiga sune wadanda muke Jin dadin sayarma da kayanmu, Kuma ni ba Dan bindiga bane, sabidda babana yasha gayaman kada in sake in shiga idan na shiga zai harbi don aikiyi bai da kyau.
Yace ” Amman nasan wadansu dayawa dake cikin garin Galadima Wanda sun shiga dajin basa fitowa sai idan zasu ga iyalansu sannan su kwashi mata suyi gaba.
Comments 2