Mai horas da Yan Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester City da ke kasar Ingila Pep Guardiola ya ce zai so ganin dan wasan gaban Ƙungiyar Sergio Aguero ya ci gaba da zama a gasar Firimiya.
Dan wasan mai shekara 32 zai yi bankwana da Etihad ne a watan Mayun gobe bayan da ya shafe shekara goma yana murza leda a Ƙungiyar.
A Yanzu haka kungiyoyin dake rige-rigen ɗaukar dan wasan sun hada da Chelsea da Tottenham har ma da Leeds United da zata kara da City a yau Asabar.
Kuma Guardiola ya ce zai yi farin ciki idan ɗan wasan ya ci gaba da zama a Ingila ht ma ya dawo yana yakar City din.
“Ina so na gan ahi cikin yanayi mai kyau, dukkanin mu kuna fatan haka, kuma kun ga yadda muka maida cikin shekaru goman shi da mu a nan.”