Inda Gwamantin PDP ce, da yanzu ta kawo ƙarshen Yajin Aikin ASUU — inji Saraki
Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai na Kasa Bukola Saraki yace bazai bari Yajin Aikin Jami’o’in Najeriya ya daɗe kamar haka ba idan da yana Shugaban Majalisar Dattijai ko kuma Shugaban Gwamnonin Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Katsina: Hukumar Kiyaye Haɗurra FRSC tace zata hukunta Direbobin da basu Balaga ba
Saraki, wanda yace rashin Jajircewa da kishi na Jam’iyyar APC Mai Mulki bazai rasa na saba da dogon yajin aikin da ASUU ke yi ba, yana mai jaddada matsayar sa a ranar Lahadi a Shafin sa na Twitter, inda yace “bazai taɓa yarda yabar yajin aikin nan ya daɗe haka ba, idan yana a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnoni ko kuma Shugaban Majalisar Dattijai. Abun da bazai taɓa yiwuwa ba.”
Saraki wanda shine tsohon Gwamnan Jahar Kwara, ya bayyana cewar a lokacin wa’adin mulkin sa a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnoni, Shugaban Majalisar Dattijai, ya tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya.
Da yake jawabi ga Manema labaru a Ilori, bayan addu’o’in Sallah yace “babu jajircewa da kishi a wajen masu mulki a yanzu. Kuma wannan shine bambancin Gwamnatin PDP da Gwamnatin yanzu.
Saraki ya kara da cewa da yawa daga cikin mutanen dake cikin PDP sun zaɓi su zauna a cikin ta, saboda ra’ayin su na samun Najeriya nagartacciya. Ya kuma bukaci ƴan Najeriya dasu zaɓi PDP a Babban Zaɓen Shekarar 2023 mai zuwa.