Bankin duniya ya sanya sunayen kasashen Sin da Indiya a sahun farko na jerin kasashen da gwamnatocinsu ke saukaka harkokin kasuwanci cikin shekarun baya-bayan nan ga al’ummomin kasashe.
Cikin rahoton da bankin na duniya ya fitar kan kasashen ‘yan gaba gaba wajen saukaka harkokin kasuwanci ga al’ummarsu, bankin ya ce duk da rikicin kasuwancin da ke ciwa Sin tuwo a kwarya hakan bai hana ta zamowa cikin jerin ‘yan goman farko da ke fafutukar saukaka kasuwanci a kasashensu ba.
Sin wadda ke matsayin ta hudu wannan ce shekara ta biyu a jere da take shiga sahun ‘yan goman farko yayin da Indiya wadda ke matsayin ta Bakwai cikin shekara ta Uku a jere da take samun wannan tagomashi, sun bar Faransa a baya wadda yanzu ta dawo matsayin ta Sha Biyar maimakon ta 35 da take a baya.
A cewar David Malpass shugaban bankin na duniya kasashen Sin da Indiya sun samar da sauye-sauyen haraji baya ga dokokin shige da fice da suka saukaka harkokin cinikayya duk da kalubalen da kasuwanci ke fuskanta a halin yanzu.
Bankin wanda ya gudanar da binciken kan yadda kasashen ke bayar da damar kasuwanci ya ce duk da yakin kasuwancin da Sin ke fuskar bai hana ta samar da sabbin tsare-tsaren da suka saukakawa ‘yan kasuwar gudanar da harkokinsu ba.
Sauran kasashen da bankin duniyar ya bayyana a masu saukaka harkokin kasuwanci akwai New Zealand a matsayin ta 1 sannan Singapore sai Hong Kong sai kuma Koriya a matsayin ta 5 da kuma Amurka a matsayin ta 6.
Sauran kasashen da bangaren kasuwancinsu ya habaka tattalin arzikinsu akwai Saudiyya Arebiya sai kuma Jordan sai Togo da Bahrain sannan Tajikistan kana Pakistan sai Kuwait da kuma Indiya sannan Nijeriya.