By Abbas Yakubu Yaura
An yi wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a jihar Uttarakhand da ke arewacin Indiya yayin da wasu ma’aurata suka kai karar dansu daya tilo da matarsa saboda rashin haifo musu jika bayan shekara shida da yin aure.
Shirin ma’auratan shine samun jikoki da zasu yi wasa da su bayan sun yi ritaya ba tare da la’akari da jinsi ba.
Afghanistan: Fashewar Wani Abu ya Jikkata Mutane 3 suna Tsaka da Sallar Juma’
An shigar da karar da ba a saba ganin irin ta ba a kan dalilai na “hazakar tunani”, amma dan da matarsa sun yi tsokaci kan batun.
Da suke ba da labarin abin da ya faru da su, Sanjeev da Sadhana Prasad sun ce sun yi amfani da kudaden da suka samu wajen renon dansu da kuma biyan kudin horar dashi dan ya zama matukin jirgin sam, da kuma bikin aure mai kayatarwa.
Prasad ya ce a shekarar 2006 ya aike da dansa zuwa kasar Amurka domin a horar da shi tukin jirgin sama kan kudi dalar Amurka 65,000.
Kuma lokacin da ya koma Indiya a shekara ta 2007, ya rasa aikinsa kuma iyayensa sun tallafa masa da kudi sama da shekaru biyu.
Sai dai daga ƙarshe Shrey Saga ya sami aiki a matsayin matukin jirgin sam.
Iyayensa sun shirya masa aure tare da Shubhangi Sinha a cikin shekarar 2016, suna fatan za su sami “jikokin da za su yi wasa da su” a lokacin da suka yi ritaya, amma sun ji kunya kasancewa shiru babu amo babu labari.
Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa ma’auratan suna neman dan ya biya su diyya ta kusan dalar Amurka 650,000 (£525,000) idan ba a haifo santalelen jika cikin shekara guda ba.