By Ishaq Dabai
Wata babbar kotu a yau Litinin, ta yankewa wani dan siyasa Dan kasar Indonesia hukuncin daurin shekaru 12 agidan yari, bayan da aka same shi da laifin cinye kudin tallafin cutar corona sama da dala miliyan ɗaya. A yayin da yake rike da mukamin ministan jin dadin jama’ar kasar ashekarar da ta gabata.
Dan siyasar mai suna Juliari Batubara an same shi da laifin karbar kudin wanda yakai Rupiah biliyan 14.6 dai dai da Dala miliyan daya, daga hannun wani kamfani da yake samar da naman kaji kuma ya haifar da barkewar annobar cutar COVID19 a kasar ta Indonesia, acewar kotun dake birnin Jakarta.
Batubara shine tsohon ma’aji na musamman a jam’iyar Ruling Indonesia Democratic Party of struggle, Wanda Kuma a dan Haka ne, ta bada umarnin da ya dawo da kudin da ya cinye. ko a kara masa hukuncin dauri na shekaru biyu.
Ya dai zauna a ofishin sa na tsawon shekaru hudu kafin daga bisani ayanke masa hukunci.
Mai gabatar da kara yace ma’aikatar ta bukaci da abiya Rupiah 10,000 kasa da Dala daya akan kowanne jaka ta abinci a yayin shirin bada tallafin COVID19 wanda darajarsa takai Rupiah tiriliyan 5.6.