Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai hamayya, a zaben 2019 Atiku Abubakar, ya mayarwa fadar shugaban kasa martani inda ya ce, kotun da ke sauraron karar da ya shigar yana kalubalantar zaben shugaba Buhari, ba ta yi watsi da bukatar da ta gabatar gaban kotun ba na a bai wa bangarensa damar bincikar kundin bayanai na Hukumar Zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ba.
Sabanin yadda mai magana da yawun shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa kotun ta yi fatali da bukatar bangaren Atiku da ya gabatar.
A cewar kakakin Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya ce kotun sauraron karar zaben ba ta ce ta yi watsi da bukatar mai gidan nasa ba, sakamakon ba a fara shari’ar gadan-gadan ba.
Kuma dama can a ka’ida sai an soma shari’a babu kama hannun yaro, sa’annan za a bayar da damar bincikar kundin bayanai na Hukumar INEC.