An bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Filato, Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana ranar Asabar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana hakan a ranar Litinin.
Shugaban hukumar ta INEC, Musa Yusuf, bayan tattara kuri’un da jam’iyyu suka samu a zaben, ya ce Mutfwang ne ya samu kuri’u mafi rinjaye inda ya doke dan takarar jam’iyyar Nentawe Yilwatda. Kamar yadda Jaridar Daily Post ta rawaito.
A Wani Labarin Kuma PDP Ta Lashe Kujeru 28 Na Majalisar Dokoki, Yayin Da APC Ta Tsira Da Hudu
Majalissar dokokin jihar Oyo ta 10 za ta kasance karkashin jam’iyyar PDP, inji rahoton jaridar DAILY POST.
Majalisar dokokin jihar tana da kujeru talatin da biyu (32).
Sakamakon da majiyar jaridar DIMOKURADIYYA ta samu a ranar Litinin din nan ya nuna cewa jam’iyyar PDP mai mulki a jihar ta lashe kujeru (28) daga cikin kujeru talatin da biyu a zaben majalisar dokokin jihar da aka gudanar ranar Asabar.