Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a jiya lahadi ta dage cigaba da tattara sakamakon zabe a jihar Adamawa har zuwa yau Litinin sakamakon takaddamar sakamakon zaben karamar hukumar Fufore, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Jami’in dake kula da tattara sakamakon zabe na jihar, Farfesa Muhammad Lamin Mele, ya sanar da sakamako daga kananan hukumomi 20 cikin 21 kafin rashin jituwa tsakanin wakilan jam’iyyar kan sahihancin sakamakon na karamar hukumar Fufore.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: INEC Ta Ayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Ogun
Wakilin jam’iyyar APC, Usman Mauludu, ya yi zargin cewa an tabka magudi a sakamakon da aka samu daga Fufore.
Daga nan sai jami’in zaben mazabar, Yunus Hudu, ya dage cigaba da bayyana sakamakon zaben zuwa karfe 12 na rana a yau duk da zanga-zangar da wakilan jam’iyyar PDP karkashin jagorancin tsohon karamin ministan lafiya, Aliyu Idi Hong suka yi, inda suka dage cewa dole ne a ci gaba da tattara sakamakon zaben.
Jami’an tsaro sun harba bindiga a saman iska da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa ‘yan baranda da suka taru a kusa da cibiyar tantara sakamakon zabe, inda suka addabi masu ababen hawa. Yan barandan sun lalata wasu motoci kadan.
A wani labarin kuma, An Sake Zaber Sanwo-Olu A Matsayin Gwamnan Jihar Legas A Karo Na Biyu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.
Sanwo-Olu na jam’iyyar ya lashe kananan hukumomi 19 cikin 20 na jihar a zaben.
Sanarwar ta fito ne cikin daren Litinin, 20 ga watan Maris, daga bakin jami’in zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki a jihar Legas, Farfesa Adenike Oladeji.