INEC ta koka kan ƙarancin masu rajistar Katin Zaɓe a Jahar Katsina
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC a Jahar Katsina ta bayyana damuwa na rashin fitowar mutane domin rajistar Katin Zaɓe na din-din-din a sabbin Akwatunan Zaɓe guda 1,750 da aka ƙirƙira.
Kwamishinan Zaɓe na Jahar Alhaji Jibril Zarewa ya bayyana haka a lokacin dayake tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa a ranar Juma’a a Katsina.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da-Dumi-Dumi: Matar Alaafin ta rasu makonni bayan rasuwar sarkin
Yace shekara ɗaya bayan fara rajistar Katin Zaɓe, amma akwai ƙarancin masu yin rajistar a sabbin Akwatuna da aka buɗe.
Zarewa yace “a watan Mayu Shekarar 2022 a lokacin da muka gudanar da wata ƙididdiga, mun gano cewa sabbin Akwatunan Zaɓe 1,750 da aka buɗe, kimanin Akwatuna 1,200 basu da sama da mutane 50 da suka yi Rajista a kowane daga ciki.
“Duk da za’a iya alaƙanta wannan da Dakatar da Layukan Sadarwa a Ƙananan Hukumomi 17 daga cikin 34 na tsawon watanni biyar sakamakon matsalar tsaro.
“Tun lokacin da muka dawo rajistar a watan Maris, cikin Akwatuna 1,750 da aka ƙirƙira, kimanin Akwatuna 1,200 basu da sama da mutane 50 da suka yi Rajista a kowane.
“Muna kira ga Al’ummar yankunan inda aka ƙirƙiri sabbin Akwatuna dasu je suyi rajista, domin INEC a shirye take a gare su.
“Dalilan samar da wannan sabbin Akwatunan Zaɓe shine su taimaki Al’ummar yankin, tare da rage yawan mutane ta hanyar canja Akwatuna zuwa wasu.”
Ya bayyana cewa da farko akwai Akwatuna 4,902 a Jahar nan, amma da ƙirkirar sabbin Akwatunan, akwai Akwatuna 6,652.
Zarewa ta bayyana cewar, abun a yaba ne yadda ake karɓar Katin Zaɓe, domin daga cikin Katin Zaɓe Miliyan 3.230, kimanin guda 50,000 kaɗai ne ba’a amsa ba.
“Ya zuwa ranar 12 ga watan Janairun Shekarar 2022, mun ɗauke dubu 53,000 daga Shalkwata, kuma ƴan kwanakin nan, mun sake ɗaukar 20,000 ga mutanen da suka yi canji,” Inji shi