Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya wato INEC za ta gudanar da sabon zaben Sanatan Kogi ta yamma tsakanin Sanata Dino Melaye na jam’iyyar PDP da Sanata Smart Adeyemi na jam’iyyar APC a ranar 16 ga watan Nuwamba, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sanar.
Hukumar INEC a wani jawabi dauke da sa hannun Mista Festus Okoye, Shugaban kwamitin bayanai na hukumar, ya bayyana cewa za a hada zaben Sanatan ne tare da na gwamnan Kogi.
Okoye, Kwamishinan zabe na kasa, a wani jawabi da ya gabatar ga manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya bayyana cewa za a kuma gudanar da zaben cike gurbi ga mazabar Sabuwa a jihar Katsina a ranar 30 ga watan Nuwwamba.