Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta ayyana ranar 19 ga watan Yuni a matsayin ranar zaben cike gurbi na yan majalisun tarayya a mazabar Gwaram ta Jihar Jigawa da kuma Sabon Gari a Jihar Kaduna.
Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Hukumar Mista Festus Okoye ya fitar, ya ce sanya ranar ta zo ne bisa sako da suk samu daga Majalisar wakilai ta wurin Kakakin ta Femi Gbajabiamila cewa kujerar dan majalisar ta Gwaram babu kowa a kai biyo bayan an mutuwar mai kujerar Yuguda Hassan Kila.
Kazalika a bangaren Jihar Kaduna ma Hukumar ta samu sanarwar cewa Kujerar dan majalisar babu kowa a kai.
A cewar Okoye Kujerar Sabon Gari a majalisar ya biyo bayan rashin halartar zaman majalasu da aka yi ta yi ne ba tare da dan majalisar ba, wanda kuma ya saɓa wa kundin tsarin mulkin kasa na 1999 sashe na 109 sakin layi 2 cikin kamar yadda aka yi wa gyaran fuska.
Daga nan sai INEC ta bukaci duk wata jam’iyya dake bukatar fafatawa a zaben da ta gaggauta mika sunayen jami’an zaben wa Jami’in zabe na karamar hukumar Sabon Gari daga kada ya wuce ranar 1 ga waan gobe, kana kuma za a rufe yakin neman zaben a ranar 17 ga watan na gobe.