By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanya ranar 26 ga watan Fabrairu domin gudanar da zabukan cike gurbi a mazabu shida na jihohi hudu.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe (IVEC), Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja a karshen taron gudanarwar.
Zabuka shida da ake shirin gudanarwa sune mazabar tarayya ta Akure Ta Arewa da Akure ta Kudu dake jihar Ondo; sai Jos ta Arewa da kuma mazabar Bassa ta tarayya dake jihar Plateau; Mazabar Pankshin ta kudu, jihar Filato; Mazabar Ngor-Okpala, jihar Imo da kuma yankin Ogoja/Yala na tarayya da kuma mazabar Akpabuyo dake jihar Cross River.
Za a gudanar da zaben ne makwanni biyu bayan an sanya ranar Asabar 12 ga watan Faburairu za a gudanar da zaben kananan hukumomin babban birnin tarayya.
Okoye ya ce hukumar za ta hada zaben mazabar jihar Ekiti ta gabas 1 da zaben gwamna a jihar wanda aka shirya gudanarwa a ranar 18 ga watan Yuni.
Sannan hukumar ta gargadi jam’iyyun siyasa kan zaben ‘yan takarar da ba su cancanta ba a zaben.
Ya bayyana cewa hukumar na tuntubar jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki da suka shafi guraben aiki a mazabar jihar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda ya kara da cewa kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna bai bayyana gurbi a mazabar jihar Giwa ta jihar Kaduna ba.
Comments 1