INEC Ta Yi Barazanar Hukunta Masu Lalata Katin Zabe.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta yi barazanar hukunta masu hannu wurin lalata katin zabe na dindindin da nufin hana ma ƴan Najeriya hakkinsu.
Ta kuma ƙara da cewa ba zata dauki batun wani faifan bidiyo dake yawo wanda ake nuna yadda ake bunne katunan zabe na dindindin a gidan wani babban mutan da wasu ba, inji majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matar data ɗauko ƴan Ta’adda suka sace Fasto, ta buƙaci Kuɗin Fansa
Hukumar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na kasa kuma shugaban sashen wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye, ta yi gargadin cewa ba za ta bari masu tayar da kayar baya su yi mata zagon kasa ba.
Saidai hukumar zaben ta ce tuni ta lalubo hanyoyin rage tulin katunan zaben dake hannun ta hanyar bada su ga masu su.
Ya ce, “an jawo hankalin hukumar kan faifan bidiyo dake yawo a yanar gizo na katunan zaben da ake zargin an binne a cikin kasa a wasu wurare, ciki har da harabar gidan wani babban mutum. Kuma ba zata dauki wannan zarge zargen da wasa ba.
Ya bayyana cewa, “sun fara gudanar da bincike kuma duk wanda aka samu da laifi a cikin wannan lamari, za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanadar.