INEC za ta ci gaba da amfani da Fasahohin Zamani don samun ingantaccen sakamakon zaɓe — Yakubu.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, ta ce za ta ci gaba amfani da fasahar zamani don samun sahihin sakamako, gabanin babban zabe na 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: An ɗaure wani mutum kan Lalata Gilashin Gidan Maƙwabcin sa watanni 8
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci Kano a ci gaba da duba aikin ci gaba da yi wa rajistar masu kada kuri’a, CVR, a faɗin ƙasar nan.
“Hukumar za ta ci gaba da zurfafa amfani da fasaha wajen zaɓe.
“Mun nuna jerin sunayen waɗanda aka yiwa rajista don ƴan Najeriya su rika sanin abubuwan da ke faruwa a INEC. Na yi imani muna da kyau.
Bayan Zabe a rumfunan zabe, za a riƙa dora sakamakon zaɓe domin ‘yan Najeriya su ga sakamakon tun kafin a kammala zaɓen,” inji shi.
Ya ce hukumar ta shawo kan ƙalubalen farko da na’urar tantancewar Bimodal Verification Accreditation, BVA.
“Muna da yakinin cewa na’urorin BVA za su yi aiki da kyau yayin zabukan 2023,” in ji shi.
Shugaban ya ce INEC za ta dauki kimanin mutane miliyan daya aiki a matsayin ma’aikatan wucin gadi domin zaɓen 2023 mai cike da hadari.
“INEC ba jam’iyyar siyasa ba ce kuma za ta tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kanta.
“INEC ba ta da dan takarar ta, sai dai abin da masu zabe ke so kuma duk abin da masu zabe suka tantance shi ne hukumar zabe za ta bayyana a karshenta,” inji shi