IPC ta bukaci Ɗaukar Mataki Ga wanda yaci Zarafin Ƴar Jarida, Nefasah Vandi
Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa (IPC) ta bukaci isasshiyar kariya ga ‘yar jaridar ABC, Nefasah Vandi wacce mijinta yaci zarafin ta a ƴan kwanan nan.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Lanre Arogundade, Babban Darakta na IPC, kuma jami’in yada labarai na IPC, Melody Akinjiyan ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Ƙungiyar Dattawan Arewa ta Caccaki Tinubu, Atiku, Obi Kan taro a Landan
A cikin sanarwar, IPC ta bayyana cewa, rahotannin da suka iso ofishinta na Kiyaye lafiyar Al’umma sun bayyana cewa, Vandi mai ‘ya’ya uku, ta sha dukan tsiya da mijin ta mai suna Ibrahim Aliyu, wanda ya sanya ta samu raunuka daban-daban, ciki har da karyewar daya daga cikin hannunta.
Arogundade, yayin da yake yin Allah wadai da harin da aka kai wa ‘yar ujaridar, ya kara da cewa yawaitar cin zarafin mata a gida da mazajensu ke yi abu ne mai ban tsoro.
Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su gudanar da bincike sosai tare da gurfanar da wanda ya aikata laifin a matsayin wani mataki na rage cin zarafi a kan ‘yan jarida mata a Najeriya.
“Mun yi Allah wadai da cin zarafi kuma muna neman a kama shi tare da yi wa wanda ake zargi da aikata laifin hukunci domin a adalci,” in ji Arogundade.
A wani labarin kuma: KASU ta yi Allah wadai da kalaman Shugaban ASUU akan Jami’o’in Jihohi