Iran ta ce lallai za ta aiwatar da hukuncin kisa kan Bafarisen nan da ya taimaka wa Amurka da leken asirin da ya kai ga kisan Babban Janar din Sojin nan na ta, bayan kotun koli ta jaddada hukuncin da aka mai tun da farko.
An yanke wa Mahmoud Mousavi Majd hukunci ne bisa laifin yin leken asiri kan sojin Iran, lamarin da ya kai ga kisan Janar Qasem Soleimani da Amurka ta yi ta wajen amfani da jirgi mai sarrafa kansa.
Rfi Hausa ya labarto cewa; an sami Majd da laifin karbar wasu makudan kudade daga hukumar leken asiri na Amurka CIA, da ta Isra’ila MOSSAD, a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron Iran.
Ma’aikatar tsaron Iran din ta ce kotun koli ta jaddada hunkuncin da aka yanke wa Majd, kuma nan ba da jimawa ba za ta aiwatar da shi.
Soleimani ne Kwamandan Dakarun Quds, wani bangare na rundunar juyin juya hali na Iran, wato Iran Revelutionary Guards, kuma Amurka ta kashe shi a kusa da filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Bagadaza a watan Janairu.