Amurka ta yi gargadin cewa kungiyar ISIS da Al-Qaeda sun soma kutsawa zuwa yankin arewa maso yammacin Nijeriya.
A watannin da suka wuce an samu karuwar hare-hare a Kaduna da Katsina da Sokoto da Zamfara da kuma wasu jihohin yankin.
A taron manema labarai, kwamandan dakarun Amurka na musamman a Afrika, Dagvin Anderson ya kara da cewa kungiyar Al-Qaeda kuma na kara fadada rassanta a yankunan kasashen yammacin Afrika.
Bbc ta labarto cewa; bayanan wadanda aka wallafa a shafin intanet a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Anderson ya ce Amurka za ta ci gaba da hada gwiwa da Najeriya domin musayar bayanan sirri.
A cewarsa hare-haren Al-Qaeda sun janwo rufe makarantu fiye da 9,000 kuma 3,000 daga ciki a kasashen Mali da Burkina Faso.