Kungiyar ‘Yan ta’addar ISIS tace itace ta gudanar da hari a kasar Sri Lanka, ta fitar da hotunan mayakanta da tace suna su kai hari a ranar Lahadin data gabata.
Harin dai da kungiyar ta kai ya hallaka mutane kimani 320 a ranar bikin murnar Ester a kasar Sri Lanka.
Wannan ne dai hari ne farko da kungiyar ta kai tin bayan da ta samu sabon shugabanci a shekarar 2014.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ta rawaito cewa kungiyar ta fitar da sanarwar daukar alhakin harin tare da bayyana sunaye da hukuma hotunan dakarunta da suka aiwatar da harin a kasar Sri Lanka.
Kungiyar dai ta kira harin da sunan “Hari mai Albarka”
Masu Alaƙa Subhanallah: Harin ta’addanci a masallacin New Zealand cikin hotuna
IS, ta fitar da sunayen Abu Obeidah, Abu Baraa da Abu Moukhtar da cewa sune suka kai hari a Otal din Shangri-La,Cinnamon Grand da Kingsbury.
Ta bayyana Abu Hamza, Abu Khalil da Abu Mohammad a matsayin wadanda suka kai harin a Cocina dake garuruwan Colombo, Negombo da Batticaloa.
Abu Abdallah shine cikon na 7, kungiyar tace shine wanda ya kashe jami’an ‘yan sanda 3 a harin Colombo Suburb.
Alkamuna sun nuna harin yana daga cikin hare-haren ta’addanci tin bayan harin 9/11 na kasar Amurka.
Sai dai tuni gwamnatin kasar ta Sri Lanka ya bayyana kungiyar National Thowheeth Jama’ath (NTJ) a matsayin kungiyar da take zargi a hannu a harin