Wata iska mai karfin gaske hade da ruwan sama ta lalata gidaje da dukiyoyi a garin Kafin Liman dake karamar hukumar Ganjuwa a Jihar Bauchi.
Dabbobi da Kayyakin amfanin yau da na dubban nairori duk sun salwanta sakamakon wannan ibtila’i da ya faru a daren jiya asabar.
Kazalika an samu rumbun adana hatsi da suka kone kurmus sakamakon iskar da ta haifar da, wanda kuma akabyi kiyasin kudinsu na dubban nairori ne.
Da yake magana sakamakon wannan jarabawa, wani mazaunin kauyen mai suna Alhaji Sa’adu wanda yana daya daga cikin wadansa suka tafka hasara, ya dangana al’amarin da jarabawa daga Allah.
Da yake jajanta wa wadanda abin ya shafa, Shugaban Karamar Hukumar Ganjuwa Alhaji Dayyabu Muhammad, ya bayyana ibtila’in a matsayin ƙaddara inda ya bukaci gwamnatin jiha da ta tagaza wa wadanda al’amarin ya shafa don rage musu radadin rayuwa.
Sau sa dama dai ana alakanta irin wannan lamari da sakacin al’umma na barin garwashin wuta yayin gama girki, lamarin dake haifar da gobara.