An harbe wata gogaggiyar ƴar jaridar kafar yada labarai ta Al Jazeera Shereen Abu Aqleh a yayin da take bayar da rahoto kan wani samame da dakarun sojin Isra’ila suka kai a birnin Jenin da ke Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Kafar yaɗa labaran mai cibiya a ƙasar Qatar ta ce sojojin Isra’ila ne suka harbe ƴar jaridar mai shekara 51 “da gangan” kuma “ba tare da ta yi wani abu ba.
Sai dai rundunar sojin Isra’ila ta ƙaryata cewa dakarunta ne suka kashe Yar jaridar.
Sun Kuma alakanta lamarin da cewa “watakila ƴan bindigar Falasɗinu ne” suka kashe ta a yayin da ake musayar wuta.
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Yair Lapid ya bayyana mutuwar Shereen a matsayin “abin takaici” ya kuma ce an ƙaddamar da binciken haɗin gwiwa tsakanin ƙasarsa da hukumomin Falasɗinu domin binciko Wanda yayi wannan aika aikar.
Ya ƙara da cewa: wajibi ne a dinga bai wa ƴan jarida kariya a yankunan da ake yaƙi.
A wani labarin Kuma na daban
Jigawa: Ƴan Majalisu sun kori Shugaban Ƙaramar Hukuma kan Ƙin Biyayya ga Shugaban APC
Majalisar Dokokin Jahar Jigawa ta kori Shugaban Ƙaramar Hukumar Yankwashi ta Jahar sakamakon zargin yaƙi yin biyayya ga Shugaban Jam’iyyar APC.
Shugaban Kwamitin Majalisar akan Yaɗa Labaru dake wakiltar Kafin Hausa Muhammad Na’im ya bayyana haka ga Manema labaru.
Yace Shugaban Ƙaramar Hukumar an kore shine saboda faɗin maganganu marasa tushe da kuma yaɗa labarin ƙarya akan Shugaban Jam’iyyar APC na Jahar Aminu Ahmed.
A cewar sa “Majalisar ta karɓi ƙorafi daga Shugaban Jam’iyyar APC yana ƙalubalantar Shugaban Ƙaramar Hukumar kan yaɗa labarun ƙarya cewa Shugaban Jam’iyyar yana karɓar kuɗaɗe ga wasu ƴan takara domin yi masu alfarma.
Ya bayyana cewa Majalisar ta kuma daɗe tana karɓar ƙorafe-ƙorafe kan lalata Dukiyar jama’a da Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi guda 8 ke yi.
“Majalisar ta kafa wani kwamiti domin yayi bincike kan Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi guda 8 da suka haɗa da Gwaram, Kafin Hausa, Guri, Miga da Birnin Kudu, da Birniwa, da Babura”, Inji shi.
Wani daga cikin Shuwagabannin Ƙananan Hukumomin wanda ya buƙaci a sakaye sunan sa ya bayyana cewa, zargin Ƙarya ne, bai faru ba.
Yace zargin kawai ba komai bane illa irin na Siyasa.