Yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar a kasar Isra’ila sakamakon sake dawowar cutar korona, kasar ta dawo da dokar tilasta sanya takunkumi a ranar juma’a.
A makon da muke ciki ne dai da ma kasar ta janye dokar bayan raguwa yawan masu dauke da cutar ta korona, to sai dai alkaluma sun sauya a yau juma’a.
Hankali ya tashi a kasar matuka bayan da ta fara samun sabbin kamuwa da cutar da suka zarce 100 ko wace rana, bayan da gwaji ya tabbatar da cewa kowa ya warke a farkon watan nan.
Ko da yake dai galibin wadanda suka kamu da cutar an alakanta su ne da sabuwar cutar da ta bulla a kasashen duniya da aka mata lakabi da Delta.
Kididdiga ya tabbatar da cewa Isra’ila na daya daga cikin kasashe yan sahun gaba da suka yi tsayuwar daka wajen ganin sun dakile cutar ta korona.