- ISWAP ta saki ma’aikacin jin ƙai bayan shafe wata biyar a hannunsu
- Rundinar soji bata ce komai ba akan batun
- Harda jami’an DSS biyu cikin waɗanda suka kuɓuta
Ƙungiyar ƴan ta’adda ta ISWAP ta saki Abubakar Idris, babban jami’i a hukumar ƴan gudun hijira ta majalissar ɗinkin duniya tare da wasu mutane tara da aka kwashe akan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
A watan Janairun wannan shekarar ne dai ƴan ya ta’addan suka ɗauke Abubakar akan hanyar shi ta zuwa Maiduguri daga Damaturu.
The cable ta wallafa cewa akwai wasu jami’an hukumar jami’an tsaro na farin kaya (DSS) ma su biyu da aka tabbatar da kuɓutarsu daga hannun ƴan ta’addan.
An dai wuce da Abubakar asibiti dake birnin Maiduguri domin a duba lafiyar sa kafin daga bisani a miƙa shi ya zuwa ga iyalanshi.
Karanta wannan: Najeriya na kan gaɓar rugujewa in ba’a ɗau mataki ba- Wole Soyinka

Haka nan akwai wani babban ɗan kasuwa Mu’azu Bawa tare da sauran mutane takwas da suka samu kuɓuta waɗanda yanzu haka jami’an tsaro ke musu wasu ƴan tambayoyi.
Han ya zuwa yanzu rundinar sojin Najeriya bata ce komai ba akan lamarin.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin jami’an hukumar soji ke ƙara matsa ƙaimi wajen ƙaddamar da hare-hare akan ƴan ta’addan na ISWAP da bokoharam.
a wani labari kuma, shugaban majalissar dattawa sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa ƴan Najeriya suna buƙatar tuwita kamar yadda tuwita take buƙatar ƙasar ta Najeriya.
Shugaban dai ya magantu ne tun bayan dakatar da shafin na tuwita da gwamnatin Najeriya tayi biyo bayan goge rubutun shugaba Muhammadu Buhari da suka yi.
Yace al’umar Najeriya nabukatar amfani da Tiwita haka itama shafin tana bukatar yan’Najeriya.
Ya kuma yi Kira da a samar da maslaha a rikinci da Gwamnatin kasarnan keyi da kamfanin Tiwita.
Lawn ya bayyana nada ra’ayinne alokacin dayake jawabi a Garin Abuja, a bikin cika shekara biyu da kafa majalissar dayake jagoranta wacce itace ta 9 a kasarnan.
Comments 1