By Ishaq Dabai
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami yace iya hukumomi tsaro ne kadai zasu iya saurarar bayan wayoyin mutane.
Ministan ya fadi hakan ne a ranar Talata yayin gudanar da shirin hukumar na shekara ta 2021 zuwa 2025 inda mataimakin shugaban hukumar gudanarwa farfesa Umar Danbatta ya fada a Abuja.
“A lokacin da muke so mu tuntubi wani sai mun bukaci kundin tsarin mulki wadanda shi zai bamu damar mu saurari bayanan sirrin na wayoyin mutane ina nufin inda sashe na 37 da kuma 39 yabada dama”.
“Iya jami’an tsaro ne kadai keda karfin ikon sauraro ko bibiyar bayanan sirrin na wayoyin mutane, mu bamu da wannan ikon, idan ba haka ba, to azaba, hakan ba dai dai bane ga kowanne mutum ya tuntubi hukumar NCC ko ma’aikatar ta bashi bayanai akan hakan”, a cewar sa.
“A lokuta da dama jami’an tsaro zasu iya fuskantar neman baya nai saboda shugaban kasa ya bada umarnin ga jami’an tsaro su saurari bayanan sirrin na wayoyin mutane batare da fuskantar wata tirjiya ba alokacin da suke aikinsu abune mai sauki su sami a bubuwa da yawa a lokacin da suka tuntubi hukumar ta NCC ko ma’aikatan su.