Kwanaki huɗu bayan an sace ƴan uwansu guda a Akure, Jahar Ondo, waɗanda suka sace su, sun sake su bayan an biya su Naira Miliyan 5 a matsayin kuɗin fansa.
Ƴan ta’addan sun sace ƴan uwan junan a cikin motar mahaifiyar su ƙirar Toyota Camry a yankin Leo ta Akure, Babban Birnin Jahar a ranar Juma’a da yamma da misalin karfe 8:30 na dare.
Wani daga cikin iyalan wanda ya tabbatar da sakin yaran ga Manema labaru, yace an sako yaran da misalin karfe 10 na dare a ranar Talata bayan an biya kuɗin fansar su.

KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Matashi Ya Hallaka Bayan Yunkurin Sata A Jikin Na’urar Taransufoma
Ya ƙara dacewa, ƴan matan guda biyu da ake kira da Fikayo da Bolu, sun samu jagorancin ƴan sanda zuwa ga iyayen su, wanda suka miƙa su.
Ya bayyana cewa ƴan matan guda biyu an ajiye su a wurin yankin Okuta Elerinla ta Akure, inda wasu masu taimako suka hange su, tare da ɗaukar su ya zuwa ga ofishin ƴan sanda.
Yace “da farko masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su Naira Miliyan 40, amma daga bisa ni aka biya Naira miliyan 5 bayan an tattauna tsakanin iyaye dasu.
Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta Rundunar Ƴan sandan Jahar Mrs Funmilayo Odunlami ta tabbatar da cewa, ƴan mata guda biyu sun shaƙi iskar ƴanci a ranar Talata da dare, bayan wasu sun kaisu a ofishin ƴan sanda.