Iyaye sun koka kan Dakatar da shirin ciyar da abincin Ƴan Makaranta a Zamfara
Iyaye da masu kula da Ɗaliban Makarantun Gwamnatin jihar Zamfara sun koka da yadda gwamnatin jihar ta dakatar da ciyar da dalibai kyauta, wanda hakan zai hana Ɗaliban shiga makarantun gwamnati.
Sun yi nuni da cewa, ciyar da yara kyauta yana da tasiri mai kyau wajen habaka ilimi, domin yana kara wa dalibai kwarin guiwa su kasance a kan lokaci a makarantun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jana’izar Sarauniya Elizabeth ta nuna Ƴan Uwantaka a Tsakanin Al’umma, Ƙasashe – Osinbajo
Sai dai wani kwakkwaran bincike da jaridar DAILY POST ta gudanar ya nuna cewa tun bayan da gwamnatin jihar ta dakatar da ciyar da daliban kyauta a makarantun, tare da matsalar rashin tsaro, adadin daliban ya ragu matuka.
Wasu daliban makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke Gusau, wadanda suka zanta da manema labarai, sun ce yanzu haka daga gidajensu suke zuwa makarantar da kayan abincin da suka shirya tun bayan da gwamnatin jihar ta yanke shawarar dakatar da ciyar da makarantun.
Sun yarda cewa wasu daliban makarantar sun daina zuwa makarantar, inda suka nuna cewa dakatarwar ba za ta rasa nasaba da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na dakatar da ciyar da daliban ba.
A cewar daya daga cikin iyaye da waliyyai, Alhaji Mohammed Adamu, gwamnatin jihar ta kafa hukumar ciyar da abinci ta jiha ne domin karfafa gwiwar matasa da su samu shiga manyan makarantun gwamnati.
“Gwamnan jihar na farko Sanata Ahmed Sani Yarima ne ya kafa hukumar a shekarar 2000 domin karfafa gwiwar dalibai su rika zuwa makarantu akai-akai.
“Shirin yana nan tun kafin gwamnati mai ci ta fara aiki, don haka babu wani dalilin da zai sa a dakatar da shirin wanda zai yi matukar tasiri a harkar ilimi a Jihar,” inji shi.
A cewarsa, dakatarwar za ta shafi masu samar da abinci ga makarantun ta fuskar tattalin arziki saboda za su kasance marasa aikin yi.
Ya kara da cewa “Mun sha tuntubar masu ruwa da tsaki da masana ilimi domin su taimaka mana wajen shawo kan gwamnatin jihar ta sake duba matakin da ta dauka domin ceto fannin ilimi.”
Adamu ya bayyana cewa ciyar da daliban kyauta ya taimaka matuka wajen jawo dimbin masu rajista a makarantun gwamnati.
“Dakatarwar ta kara yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar saboda dalibai da yawa ba sa son komawa makarantunsu,” in ji shi.
A wani labarin kuma: Manomi Ya Nutse a Ruwa, Yayin da Mutane 8 Suka tsira a Hatsarin Kwale-kwale
Wani bala’i ya afku a ranar Lahadi a unguwar Kabala Doki da ke karamar hukumar Kaduna ta Arewa, yayin da wani manomi ya nutse a ruwa tare da wasu mutum takwas da suka tsira daga hatsarin kwale-kwale a jihar.
Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Lahadi inda wanda abin ya shafa, mai suna Umar, ya taka kwale-kwalen domin taimakawa mutanen da suka makale a gefen kogin amma kwale-kwalen ya kife.