Iyayen yaran da aka sace guda 118 daga Kano a shekarun baya, sun zargi gwamnatin jihar da rashin tabuka komai wajen kubutar da ‘ya’yan nasu.
A yayin wata zanga-zangar lumana da suka gudanar zuwa hukumar karbar korafe-korafen ta jihar Kano, iyayen yaran mata sunce ko kadan ba su gamsu da aikin kwamitin da Gwamnati ta kafa akan batun ba.