Iyorchia Ayu ya zama shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, wanda hakan ya kawo ƙarshen zaɓen shuwagabannin Jami’iyyar da safiyar ranar Lahadi.
Tsohon shugaban Majalisar Dattijan shine ya samu nasara a matsayin ɗan takarar da aka zaɓa ta hanyar sasanci daga Shuwagabannin PDP a Arewa.
Amma duk da haka, sai da aka kaɗa ƙuri’a, inda kimanin masu zaɓen dubu 3,511 suka gudanar da zaɓen na ƙasa.
Haka zalika, masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen an fara kiran na Jahar Abia da Adamawa, a yayinda Abia nada ƙuri’a 116, sai Adamawa nada 118.

KARANTA WANNAN LABARIN: Ba mu da cutar Shan-inna A Cewar Gwamnatin Jihar Adamawa
A cewar Shugaban Tsare-tsare zaɓen shuwagabannin Jami’iyyar na Ƙasa kuma Gwamnan Jahar Adamawa Alhaji Umaru Fintiri, akwai kimanin masu kaɗa ƙuri’a 3,701an tantance 3,511 daga cikin su.
Ga jerin ƴan takarar da akayi sasanci, suka zama zaɓaɓɓu a lokacin zaɓen
Iyorchia Ayu – Shugaban Jam’iyya na Ƙasa
Umar Illiya Damagum -Mataimakin Shugaba na Shiyyar Arewa
Taofeek Arapaja- mataimakin shugaban na Shiyyar Kudu
Samuel Anyanwu – Sakataren Jam’iyyar
Ahmed Yayari – Ma’aji
Umar Bature- Mai tsare-tsaren jamiyyar
Daniel Woyegikuro – Sakataren Kuɗi
Stella Effah-Attoe – Shugabar Mata
Mohammed Kadade Suleiman – Shugaban Matasa
Kamaldeen Adeyemi Ajibade – Mai bada Shawara ta fuskar Shari’a
Da sauran su.