Jahar Delta ta rufe Makarantar da Ɗalibi mai watanni 19 ya mutu, bayan Dukan Malami
Gwamnatin Jahar Delta ta kulle Makarantar Firamare da Nazare, Asaba, bayan zargin Malamin da dukan Ɗalibo mai watanni 19 da yayi sanadiyyar mutuwar ta.
Malamin mai suna Emeka Nwogbo wanda ɗan gidan mai mallakin makarantar an samu rahoton cewa ya doke shi mai suna Obinna Udeze a ranar Litinin 7 ga watan Fabrairu na shekarar 2022, tare da barin shi da tabo a jikinshi na dukan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kannywood: Shahararren Jarumi Naziru Sarkin Waka Ya Baiwa Ladin Cima Kyautar Naira Miliyan Biyu
Ƙaramin yaron ya mutu ne a Asibitin Ƙwararru dake Asaba a ranar Asabar 12 ga watan Fabrairu, sakamakon dukan shi.
Amma Kwamishinan Ilmin Makarantun Firamare Chika Ossai ya shaida cewa a ranar Lahadi Gwamnati ta kulle Makarantar.
Yace “dagaske, a ranar Lahadin nan da safe Gwamnati ta shiga lamarin, tare da kulle Makarantar daga yanzu, abu na biyu Bama a amince da Makarantar.
“Mai makarantar da ɗan ta suna a kurkukun ƴan sanda, gwamnati ta damu da lamarin sosai, kuma zata bishi har ƙarshe, domin tabbatar da cewa waɗanda suke buɗe makarantu ba bisa ƙa’ida ba an magance su.
“Abune mai sauƙi ka duba Makarantun da aka yiwa rajista, amma wanda ba bisa ƙa’ida ba, zamu cigaba da kulle su.
Comments 1