Jahar Edo ta Tabbatar da Mutane 8 da suka kamu da Cutar Ƙyandar Biri
Kwamishinan lafiya na jihar Edo, Farfesa Akoria Obehi, a ranar Litinin ya bayyana cewa kawo yanzu mutane takwas sun kamu da cutar Ƙyandar Biri a Jihar.
Farfesa Obehi wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin, ya ce duk mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun warke.
KARANTA WANNAN LABARIN: A ƙarshe da sai na murƙushe Ƴan ta’adda kafin in bar Ofis a 2023 – Buhari
“A cikin karuwar adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ta Ƙyandar Biri a Edo, ya zama wajibi a yi gargadi kan hadarin kiwon lafiya da kwayar cutar ke haifarwa tare da sake jaddada bukatar mazauna yankin su yi taka tsantsan tare da bin matakan lafiya.”
Ta bayyana alamun cutar kyandar biri da suka haɗa da zazzabi, ciwon kai, raunin jiki, ciwon makogwaro, da kara girma a ƙarƙashin muƙamuƙi da wuya.
“Haka kuma yana iya zuwa da bayyanar kurji a fuska, tafin hannu, tafin qafa, al’aura, da sauran sassan jiki, wanda zai iya fitowa da qarfi ko mai cike da ruwa a farkon farawa kuma zai iya bayyana cikin lokaci biyu, zuwa makonni uku bayan kamuwa da cutar, ya danganta da yanayin lafiyar mutum.
Ta shawarci mazauna yankin da su guji cuɗanya da matattu ko namun daji kamar ƙananan dabbobi masu shayarwa da suka haɗa da ɓeraye.
Ta kara da cewa mutane su dafa duk abincin da ke dauke da naman dabbobi sosai kafin su ci; guje wa cudanya mara kariya da dabbobi masu kamuwa da cuta, da mutane, a wanke hannu akai-akai kuma a yi amfani da sinadarin tsaftace hannu a lokacin da babu ruwa