Gwamnatin Plateau ta bankaɗo ma’aikatan da su ka yi ritaya da matattu 413 da ke ci gaba da karɓar albashi
Gwamnatin Jihar Plateau ta bankaɗo ma’aikatan da su ka kammala shekarun su na aiki, da waɗanda su ka rasu, har ma da waɗanda lokacin ritayar su ya yi amma har yanzu su na karbar albashi har guda 413.
Gwamnatin ta ce ba za ta yi wata-wata ba za ta cire su da ga kan tsarin albashinta.
Shugaban Ma’aikata na jihar, Sunday Hyat ne ya baiyana haka a wajen taron majalisar zartsawa na mako-mako a jiya Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Kamfanin Wasanni a Birtaniya ya zo neman ƴan ƙwallon ƙafa a Jahar Kano
Ya ce gwamnati za ta ɗauki matakin ne bayan da kwamitin binciken hada-hadar kuɗi ta ma’aikata da tantance su ya mika rahoton sa a ranar 21 ga watan Maris.
Ya baiyana cewa rahoton da kwamitin ya mika wa gwamnatin ya baiyana cewa har yanzu a kwai sunayen su a kan takardun karagar albashi tsawon lokaci.
Ya kuma ƙara da cewa an samu waɗanda su ka kai minzalin yin ritaya amma sai su ka canja takardun su domin su ci gaba da aiki.
Hyat ya ce wannan yunƙurin zai tsaftace harkar aikin gwamnati domin a samu nagarta da kuma samun damar sararin ɗaukar ma’aikata.