Ɗan takarar Gwamnan Jahar Kaduna, kuma Sanata mai Wakiltar Kaduna ta Tsakiya Sanata Uba Sani, yasha alwashin shimfiɗa ɗumbin ayyukan cigaba, idan aka zaɓe shi ya zama Gwamnan Jahar Kaduna.
Sanata Uba sani ya bayyana Hakan a lokacin da ya Kai ziyara ga Majalisar Dokokin Jahar Kaduna a ƙoƙarin sa na tuntubar masu ruwa da tsaki na jihar Kaduna a ƙudirin sa na neman zama Gwamnan jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Sanda na Neman na Hannun Daman Shekarau, Bashir Gentile a Kano
Uba Sani wanda ya Kasance Sanatan Kaduna ne ya bayyana Jindaɗinsa ga irin kyakkyawar tarbar da Ƴan Majalisar suka yi mashi, tare goyon bayan da suka nuna mashi.
Sanata Uba sani Yace “A yau na ziyarci Majalisar Dokokin jihar Kaduna domin neman goyon bayan ku kan ƙudirin da nake dashi na neman takarar Gwamnan Jahar Kaduna, domin yiwa al’ummar jihar Kaduna hidima idan na zama gwamna”.
Na shaida wa ’yan uwa masu Kima da daraja cewa burina ya samo asali ne domin ci gaba da gina ayyukan manyan abubuwan da Gwamnan mu Malam Nasir El-Rufai Dole ne a kai jihar Kaduna zuwa wani mataki na girma wanda yanzu ta kama hanya Kuma ba zamu bari jihar ta koma baya ba.
“A matsayina na ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin jihar Kaduna, ya zama wajibi na tuntube ku da neman albarka da goyon baya gami da Jan hankali tare da aiki a tare domin cigaban Al’ummar jihar kaduna”. Inji Sanatan
Shugaban Majalisar Dokokin Jahar Kaduna Hon. Tajudeen Abass ya bayyana Jindaɗinsa na yadda ɗaya daga cikin masu wakiltar Al’ummar a majalisar, ya kasance kan gaba a takarar Gwamnan Jahar Kaduna.
Hon. Tajudeen Abbas sun sha alƙawarin za su haɗa kan mambobinsa domin su taka rawar gani domin amfanin jihar da al’ummarta.
Sanata Uba sani wanda ya kasance ɗaya daga cikin na hannun daman Gwamna Malam Nasiru Ahmad El rufa’i, kuma mafi ƙarfi a cikin ƴan takarar dake Jihar Kaduna, kuma a halin yanzu tauraruwarsa na cigaba da haskawa.
Comments 1