Bayan kira daga ɓangarori da dama ga Gwamnatin Jahar Kano akan ta taka burki ga sana’ar bara barkatai akan titi, Gwamnatin Jahar ta shirya kafa hukumar hana bara akan titi tare da hadin gwuiwa da kungiyoyin fararen hula.
Gwamnan Jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar baƙuncin shuwagabancin haɗaɗɗiyar ƙungiyar fararen hula ta jahar, a wata ziyara a lokacin taron Majalisar Zartaswa ta jahar, a ranar Talata a gidan Gwamnatin Jahar.
Tawagar ta samu jagorancin Malam Ibrahim Waiya, wanda ya jagoranci sauran shuwagabannin ƙungiyoyin daban-daban, domin su ƙara yin kira akan yawon barace-barace akan titi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shirme ne wani ya zauna a Lagos ko Port Harcourt, yace dole a miƙa ragamar shugabancin ƙasar ga Kudu — Cewar El-Rufa’i
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na Gwamnan Abba Anwar ya fitar, a ranar 26 ga watan Satumba na Shekarar 2021.
Gwamna Ganduje yace “za’a samar da hukuma da ma’aikata da zasu duba al’amarin bara akan titi. Domin bazamu iya rike hannun mu ba, muga rayuwar ƙananan yara da basu san komai ba, an ɓata ta, ta hanyar wannan matsalar barace-barace.
Ya jaddada cewa, yawon barace-barace cin zarafin ƙananan yara ne, wanda ya bayyana a matsayin abinda yake hana yaran karatun addini da ilmin zamani.
A lokacin da yake yabawa da irin damuwa da ƙungiyoyin fararen hular suka nuna, ya bada tabbacin cewa, gwamnatin jahar zata tafi da kowa da kowa, domin samun nasarar gudanar da wannan tsari na hana yawon barace-barace akan titi.
“Muna farin cikin ƙarbar ku, kuma muna godiya da damuwa da kuke yawan nuna wa. Gaskiyane cewa, dole mu samo wasu dabaru da za’ayi amfani dasu wajen kula da matsalar,” inji shi.
Tunda Farko, haɗaɗɗiyar ƙungiyar fararen hular sun turowa gwamnan takarda, inda suke buƙatar da a haɗa hannu dasu domin samun nasarar kafa doka akan hana yawon barace-barace.
An turo takardar a ƙarƙashin inuwar haɗaɗɗiyar ƙungiyar fararen hular mai kwanan wata 23 ga watan Satumba na shekarar 2021, mai taken “kira na gaggawa akan dokar hana bara a jahar Kano
tare da sa hannun Ibrahim Waiya da Peter Hassan Tijjani
A matsayina na Gwamna ina mai tabbatar maku da cewa takarda
tayi dai-dai da abinda ke cikin zuciyar mu akan hakan.