Sananniyar Ƙungiyar nan Mai suna Nagge-Daɗi Goma ta bada kyautar littattafan Karatu 280,000 ga Gwamnatin Jahar Katsina domin mara mata baya a ƙoƙarin ta na inganta ilmi.
Dayake gabatar da Littattafan ga Gwamna Aminu Bello Masari a ranar Laraba a Katsina, Shugaban Gidauniyar Babangida Inuwa, yace wannan taimakon na ɗaya daga cikin gudunmuwar da suke bayarwa a faɗin Jahar.
Ya bayyana cewar, Gidauniyar ta bada irin wannan gudunmuwar ga Mata da Ƙananan Yara da Marasa Ƙarfi a Jahar domin taimaka masu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben 2023: Ku shirya karbar ragamar jagoranci Najeriya— Yahaya Bello ga matasa
“Mun gina Famfunan Tuƙa-tuƙa da dama a Jahar Katsina, kuma mun tallafama Mata 1,500 da Naira Dubu 30,000 kowanen su.
“Ilmi wani ɓangare ne da muka baiwa fifiko, shiyasa muka bayar da Littattafan Rubutu Dubu 280,000 domin inganta koyo a Jahar Katsina.
“Muna yin haɗin gwuiwa da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) domin magance matsalar shan miyagun ƙwayoyi a Jahar Katsina,” inji shi.
A jawabin shi, Gwamna Aminu Bello Masari ya godewa Gidauniyar da wannan taimako, inda ya ƙara dacewa irin gudunmawar da suke bada wa, musamman baiwa Ilmi fifiko na Yara a Jahar abun ayaba ne.
Daganan sai ya buƙaci masu hannu da shuni dasu taimaka a ɓangaren ilmi, domin shi kaɗai ne makamin da za’a iya magance matsalolin tsaro da shan miyagun ƙwayoyi dake fuskantar Jahar.
Gwamnan ya jaddada cewa ilmi kaɗai ne zai taimakawa Gwamnati wajen magance matsalolin mahalli da yawan Jama’a ya haifar a Jahar.
Ya kuma yi kira ga iyaye, Malamai da su cigaba da kula domin ganin kyakkyawan kula da ɗiyansu suke yi da littattafan da aka basu a Makaranta, idan ya kasance suna gida.