Kwamishinan Lafiya na Jahar Lagos Akin Abayomi yace akwai raguwar yawaitar masu kamuwa da cutar Covid-19 a Jahar.
Kwamishinan ya bayyana adadin yawan waɗanda suka kamu da cutar Covid-19 a ranar Laraba.
A cewar sanarwar daya fitar, ana samun raguwar masu kamuwa da cutar daga ranar da aka shiga cutar kashi na huɗu, wanda hakan ya bayyana cewa “anzo ƙarshen kashi na huɗu na cutar”.
“Adadin masu kamuwar ya ragu daga kashi 29.3 a ranar 21 ga watan Disamba na Shekarar 2021 zuwa kashi 0.5 a ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2022. Yawan mutanen da suka kamu a yanzu sun kai 98,977,” inji sanarwar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NDLEA Ta Kama Mawakan Zinoleesky, Mohbad, Tare Da Kwato Kwayoyi
Bayanan sun bayyana cewar kimanin mutane Miliyan 1,087,835 aka gwada a Jahar, inda kashi 80 aka yishi a Asibitocin Ƴan Kasuwa, da kashi 20 aka yishi a Asibitocin Gwamnati.
Ya bayyana cewar, yawan gadajen da ake kwantawa a Asibitocin Gwamnati dana Ƴan Kasuwa ya ragu sosai.
Ya zuwa ranar 22 ga watan Fabrairu, Najeriya nada mutane dubu ɗari 254,352, a yayinda mutane dubu 230,846 suka warke, da mutuwar mutane dubu 3,142, a cewar Hukumar Kula da Manyan Cututtuka ta Ƙasa (NCDC).
A cewar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) an tabbatar da sama da mutane miliyan 11.1 waɗanda suka kamu da cutar a Afrika, da fiye da mutane 10.4 da suka warke, gami da mutuwar mutane 247,000 gaba ɗaya.