Jahar Plateau Ta Ƙwace Lasisin Duk Makarantun Firamare, Sakandare masu zaman kansu
Gwamnatin Filato ta kwace lasisin dukkan makarantun Nursery, Firamare da Sakandare a jihar.
Kwamishiniyar ilimi ta jihar, Elizabeth Wampum, ta bayyana hakan a wani taron Manema Labarai a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: ASUU: Malaman Kaduna sun Watsar da Maganar El-Rufai, Sun ƙi duba Jarrabawa
A cewar kwamishinan, an dauki matakin ne bayan gano cewa sama da Makarantu masu zaman kansu 5000 ne ke gudanar da ayyukansu ba tare da lasisi ba.
Ta ce kashi 90% na makarantu masu zaman kansu a Filato ba sa bin ka’idoji na Gwamnati, inda ta ce kashi 85% na Makarantun masu zaman kansu, 495 aka ba da lasisi a baya .
Ta ce, “Wannan shine don sanar da jama’a cewa lasisi na duk makarantun Nursery, Firamare, Ƙaramar Sakandare da Babbar Sakandare a jihar za su sake sabunta takardar shaidarsu.”
Sai dai kwamishinan ya ce an gudanar da atisayen ne domin duba yawaitar makarantu masu zaman kansu da ba su dace ba da kuma tallafa wa wadanda ke gudanar da aiki bisa tsarin doka, domin a samu ilimi mai inganci ga kowa da kowa.