Gwamnatin Jahar Zamfara ta buɗe wasu kasuwannin sati, waɗanda aka kulle wasu watanni da suka gabata, sakamakon matsalar yanayin tsaro, amma ta hana saida dabbobi a dukkanin kasuwannin.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labaru Alhaji Ibrahim Magaji Dosara ya fitar, yace an buɗe kasuwannin sakamakon yanayin tsaro daya inganta, gami da roƙo da al’umma suka daɗe suna yi.
Kwamishinan yace “biyo bayan samun rahotanni akan kwanciyar hankali a wasu sassan jahar, da roƙo da yawa da al’umma suka yi na a buɗe masu kasuwannin su, Gwamnatin jahar ta lura da hakan, ta kuma amince da buɗe wasu kasuwannin sati, da zai fara daga ranar Litinin 1 ga watan Nuwamba na Shekarar 2021.”

KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Ba Su Da Motoci, Man Fetur, Na’urorin Sadarwa, Amma Sun Amshi Billiyan 58.9 cikin Shekara 6
Kasuwannin sun ƙunshi ta Nasarawa dake Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, da Talata-Marafa a cikin ƙaramar hukumar Talata-Mafara, da Kasuwar Gusau a cikin Ƙaramar Hukumar Gusau, gami da kasuwar Shinkafi a cikin Ƙaramar Hukumar Shinkafi.
Sauran sun haɗa da; Kasuwar Daji a cikin Ƙaramar Hukumar Ƙaura-Namoda, da Nassarawa Godel a cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji, da kuma Ɗan jibga a cikin Ƙaramar Hukumar Tsafe.
“Gwamnatin Jahar bata amince da buɗe kasuwar dabbobi wato-Kara a dukkanin kasuwannin.
“Gwamnatin na kuma gargaɗi akan duk wani rikici da ka’iya haifar da karya doka da oda a cikin kasuwannin,” inji Kwamishinan.