Shafin sada zumunta na WhatsAPP ya tsawaita wa’adin da ya ba masu mu’amala da shi na amincewa da mika bayanan sirrinsu.
Shafin ya ɓullo da wasu sabbin sharuɗɗa ne da suka shafi bayanan sirrin mutane.
Miliyoyin masu amfani da shafin a fadin duniya ne suka yi wa wannan shiri tutsu, har ma suka koma amfani da wasu shafukan masu hamayya da Whatsapp kamar Signal da Telegram.
A kwanan nan ne Telegram ya ce yawan masu amfani da shi sun hau miliyan 500, kuma ya ƙara samun jama’a daga masu ficewa daga WhatsApp
Yanzu kamfanin ya tsawaita wa’adin amincewa da sharaɗin daga ranar 18 ga wannan wata zuwa 15 ga watan Mayu, domin abokan hulɗarsa su samu damar yin nazari, ko kuma ya daina aiki a wayoyinsu idan sun ƙi amincewa.