Gamayyar ƙungiyoyin masu buƙata ta musamman ta ƙasa, sun nuna rashin jin daɗin su na yanayin da ƙasar nan take ciki musamman ma na tsadar rayuwa da halin ko in kula da matsantawa ga masu buƙata ta musamman da ake yi ba tare da samar musu da mafita ba.
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyar APC ta ƙasa na masu buƙata ta musamman Yarima Sulaiman Ibrahim ne ya bayyana hakan a wani taro da suka gudanar don bayyana ƙalubalen da suke fuskanta.
Yarima Sulaiman, ya ƙara da cewa bai kamata ace gwamnatin da suka kyautatawa zato za ta yi halin ko in kula dasu ba, musamman yadda ake kama masu buƙata ta musamman a jihohi da dama na ƙasar nan, ciki har da rusa musu muhallan su da gwamnatin jihar Kaduna ta yi a baya bayan nan.
Shima a nasa jawabin, sakataren ƙungiyar Ahmad Idris ya ce, a yanzu da dama daga cikin masu buƙata ta musamman sun kama sana’o’in dogaro da kai don kaucewa yawon bara amma duk da hakan bai hana su fuskantar tsangwama da kame su ba musamman ma a birnin tarayya Abuja.
Gamayyar ƙungiyar suna fatan gwamnati ta waiwaye su tare da duba buƙatunsu, wanda ƙin yin hakan zai tilasta su fito su yi zanga-zanga da yin addu’a ta Alƙunutu ga dukkan gwamnatoci a kowanne matakai.