Hukumar dake tsara Jarabawar samun gurbin shiga makarantun Jami’a, sun sanar da sakin sakamakon Jarabawar dalibai dubu sha hudu da dari shida da ashirin da ake bincike kan Jarabawarsu. Jaridar Thisday ta wallafa a shafinta
Mai magana da yawun hukumar ta JAMB, Dr Fabian Benjamin, ya sanar da haka a ranar Talata, inda yace an soke sakamakon Jarabawar dalibai sha hudu.
Wadanda aka soke masu sakamakon Jarabawar sun hada da, Gabriel Michael, Lawson Ruth Joy, Sadiq Mahbub Auwal, Attama Lawrence Ikedichukwu, Tambaya Yahaya, Anowa Anointing, Ogbonna Joseph Dibia, Ani Maryrose AdaLoki, Loiki Ayomiposi Precious, Ekeocha Chinecherem Michael, Oluwarotimi Toluwanimi Ayanfeoluwa, Edu Teslim Abiola, Simon Friday Promise da Onyeama Odi.
KARANTA:- Sakataren gwamnatin tarayya Tijjani Umar ya gargadi sabbin ma’aikatan 42 da su rike sirri.
Haryanzu da akwai sakamakon Jarabawar dalibai casa’in da uku wadanda suma ba’a saki ba, suna kan bincike.
Kamar yadda rahoton yazo, yace wannan ya biyo bayan amincewa da masu bincike a hukumar sukayi bayan sun gudanar da wani taro a ranar Talata 27 ga watan July, 2021.
Idan baku manta ba, a tun lokacin da hukumar ta saki sakamakon Jarabawar na farko tace akwai sakamakon wasu dalibai wadanda ba’a saki ba suna kan bincike a kansu.
Cikin wadanda aka rikewa sakamakon nasu an gano sha uku daga cikinsu sunyi satar amsa, inda an kori dalibi daya tun daga farko wanda ya bada jumillan dalibai sha hudu kenan aka kora.
A wani labarin
Yan bindiga sun shiga Kauyen Zurmi sun raunata Mutane uku sun kwashe shanu da dama
Yan bindiga sun afka cikin garin Zurmi wata Karamar hukumar ce dake Zamfara, inda suka jikkata mutane uku, sannan suka tafi da garken shanu wanda ba’a san adadinsu ba.
Sun kuma shiga Kauyen Jaye dake karkashin Karamar hukumar Zurmi dake Jahar Zamfara.
Yan bindiga dai sun afkawa garin ne da nufin hallaka mutane sannan da lalata kayayyaki su, tare da tafiya da duk wanda suka samu, sai dai Yan Sakai sun fatattake su.
Wani shaidar gani da ido ya bayyanawa gidan talabijin na Tvcnews cewa, a yanzu haka ana cigaba da kula da wadanda suka samu raunika a wani asibitin da ba’a bayyana sunansa ba.
A wancan satin dai kauyukan dake Karamar hukumar ta Zurmi, sun sha addaba wajan Yan ta’addan.
Jaridar Tvcnews, tayi kokarin samu wani rahoton daga bakin kwamishinan Ƴansandan na Jahar amman abun yaci tura, bai dauki kiran ba.
Comments 1