Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sikandire JAMB ta tsawaita rijistar jarrabawar ta shekarar 2023 da mako guda.
An sanar da tsarin tsawaita wa’adin ne daga ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, 2023.
KU KARANTA: Jam’iyyar YPP Ta Hade Guri Daya Da PDP A Filato
Yanzu haka dai siyar da ePINs zai ƙare a ranar 20 ga Fabrairu, 2023, yayin da rajistar UTME zai ƙare ranar Laraba, 22 ga Fabrairu, 2023.
Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar JAMB, Dr Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa, “A karshen sayar da e-PINs a ranar Talata, 14 ga Fabrairu, 2023, kuma dalibai 1,527,068 sun yi nasarar yin rajistar yanzu haka.
”Sai kuma 168,748, wadanda suka nuna sha’awarsu ta daukar Mock-UTME.”
Kimanin ‘yan takara 1,527,068 ne suka yi nasarar yin rijistar jarabawar UTME ta shekarar 2023.
A wani labarin kuma: Wike, Gwamnonin G-5 ba zasu iya hana nasarar Atiku ba – Segun Showunmi
Wani Jigo a Jam’iyyar PDP a Jihar Ogun Segun Showunmi ya bayyana Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike da takwarorin sa na G5, basu da ikon hana nasarar Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Alhaji Atiku Abubakar a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu.
Showunmi yace Gwamnonin G-5, sun makance, suyi tunanin cewa, zasu iya hana ko su sanya ayi wani abu da ƙuri’un mabiyan su.