By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Lahadi ne aka kama wasu mutane biyu da ake zargin matsafa ne, wadanda suka hadar da Wasiu Omonose mai shekaru 35 da Akanbi Ibrahim dan shekara 32 dauke da kan bil’adama da kuma wuyan hannu a jihar Kwara.
‘Yan sanda sun kama su ne a hanyar Oke Oyi/Jebba a lokacin da suke kan babur suna yun kurin zuwa mafakar da suke aikata tsafe-tsafen nasu.
Sarki Oba Adeyemi Ya Wakilci Al’adun Gargajiya Na Kabilar Yarbawa – Shugaban Majalisar Dattawa Lawan
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara,SP Ajayi Okasanmi yace wadanda ake zargin sun yi yunkurin kubucewa jami’an ne a yayin da suke aikin bincike a lokacin da aka kama su.
“Ayyukan da suka yi ya sa aka fara zargin masu aikata laifine, inda jami’an suka yi musu fata-fata.
“An samu wata jaka dauke da sabon kan bil’adama da kuma wuyan hannu a hannunsu,” in ji Okasanmi.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun fito ne daga Share a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.
Sannan ya kara da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa suna kai kayan ne zuwa ga wani Alfa da ke Ilorin domin gudanar da ayyukan tsubbu.
Comments 1