Hukumar dake kula da shige da fice na kayayyaki watau NCS, tace tayi nasarar kwace Motoci guda sha uku da buhunan shinkafa guda dari uku da sha hudu da sauran kayayyaki da suka kai kimanin kudade miliyan sittin a Jahar katsina a tsakanin takwas ga watan July zuwa hudu ga watan Agusta. Kamar yadda Jaridar Pmnews ta wallafa a shafinta
Shugaban hukumar ta Custom reshen Jahar Katsina Malam Dalha Wada, ya bayyana haka ga manema labarai a Kaduna a lokacin da yake bayyana nasarorin hukumar.
Kamar yadda Malam Dalha Wada, ya bayyana, yace a karkashin jagorancinsa, anyi nasarar kama Lexus Saloon 2011 mai DPV da yakai miliyan uku da digo shida, sannan an kama Toyota Corolla 2015 mai DPV da yakai sama da miliyan bakwai.
KARANTA:- DA WALAKIN: Gwamnan Legas ya ziyarci Tinubu a Landan
Sauran motocin da aka kwace sun hada da Mercedes 180 1998 model da takai N1.8 million, Mercedes C230, 2006 model mai DPV N2.3 million da Peugeot 504 guda biyu da suka kai N135,000 kowane.
Mun kuma kwace Peugeot J5 b data kai N1.4 million, da kuma wata irinta J5 bus data kai N1.6 million, da Ford van F150 1996 data kai N2 million da kuma Peugeot J5 Iveco mai DPV data kai N2.1 million.
Hakan kuma hukumar ta kwace Dab truck tipper data kai N8.1 million, Toyota Rav 4 data kai N4.3, da Toyota Highlander data kai N7.1 million” kamar yadda Wada ya bayyana.
Inda Malam Wada ya hada jimillan Motoci da aka kwace sun Kai kimanin miliyan arba’in da biyu da digo daya.
Ya cigaba da cewa hukumar ta kwace buhunan shinkafa 314 ya waje da yakai kimanin miliyan bakwai, da kuma galan Mai na 25 lita guda dari biyu da ashirin da bakwai da suka kai kimanin kudi miliyan biyar da digo hudu, sannan da kwalin taliya spaghetti guda dari da saba’in da takwas da suka kai kimanin dubu dari tara da sittin da daya.
Shugaban hukumar ta Custom na Kasa ya yabawa jami’an ka irin kokarin da sukeyi don dakile shige da fice na haramtattun kayayyaki, ya kuma basu shawarwari dasu cigaba da wannan aikin don ciyar da Kasar gaba.