By Ishaq Dabai
Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta jihar Filato DSS a ranar Laraba ta kai samame kan masu aikata barna da barayin kadarorin jirgin kasa.
DSS a cewar mataimakin daraktan ayyukan ta Garba Audu, yace akwai wani sufeto dan sanda mai murabus, wanda suka fara kama shi a daren ranar Talata yana tukin abin hawa tare da ci gaba da bincike inda ya kai samamen nasu har shagunan su dake Bukuru a karamar hukumar Jos ta kudu a jihar Filato.
Yace kayayyakin da aka kwato manyan motoci ne na jiragen kasa guda shida, da wayoyi guda 18.Yace shagon da aka kwaso kayan yana bayan ‘B’ Division na ‘yan sandan Najeriya Bukuru.
Baya da haka yace wani dan sanda mai mukamin Sajan mai kula da tashar jirgin kasa ta Bukuru, da kuma wani ma’aikacin Kamfanin Jirgin Ruwa na Najeriya, wanda shi ne mai kula da sashen na’urorin inda yace wurin zai ci gaba da zama a rufe yayin da jami’an DSS keci gaba da aikin su.
“Sufeto‘ yan sanda mai ritaya Garba Audu, da wasu mutane biyar an cafke su.An kuma kama manajan sashin tashar jirgin kasa na Bukuru, ”inji shi.