Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun yi wa gidan tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha kawanya a Abuja.
Wakilin Jaridar Dialy Trust wanda a yanzu haka yake gidan ya kuma lura da yadda jami’an ‘yan sandan Najeriya dauke da makamai Suma suka zagaye gidan
Wata majiya a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ce a ranar Talata Okorocha ya yi watsi da gayyata da dama da aka yi masa kan zargin almundahana da ake yi masa.
Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, bai amsa kiran waya da dama da wakilin Jaridar Daily Truat ya yi masa ba.
A watan Janairu ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta tuhumi Sanatan bisa zargin hada baki da wasu wajen sace Naira biliyan 2.9 daga asusun gwamnati.
FCC ta shigar da karar ne a babbar kotun tarayya dake Abuja.
Baya ga Mista Okorocha, sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Anyim Nyerere Chinenye, Kamfanonin Naphtali International Limited, Perfect Finish Multi Projects Limited, Consolid Projects Consulting Limited, Pramif International Limited, da Legend World Concepts Limited.
An shigar da tuhumar ne a daidai lokacin da Okorocha ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.