Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta cafke wata mota ƙirar Tirela maƙare da Giya, lokacin da ake shirin Kaita masaukinta a Jihar Kano.
Jami’an hukumar KAROTA ne suka sami nasarar cafke motar, lokacin da Direban ke yunƙurin shigowa cikin jihar Kano da misalin karfe 3:00na dare
An kama motar ne a kan titin zuwa Katsina kusa da kasuwar Dawanau lokacin da Direban motar ke yunƙurin shigowa cikin Kano bayan da ya sauya hanyar da ya saba shigowa ta kan titin zuwa Zariya duba da yadda hukumar ta ƙara baza jami’anta a kan titin, hakan ta sa suka canja hanyar shigowa cikin Kano kamar yadda hukumar ta sami rahoton sirri.
Bayan da aka cafke motar ne sai Direban ya tsere tare da barin motar wadda take maƙare da Giya a cikinta.
KARANTA ANAN: Nagartar Malam Shekarau Ce Tasa Muke Da Tabbaci Akansa A PDP – Makarfi
Shugaban hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗan’agundi ya yaba da ƙoƙarin jami’an da suka sami nasarar cafke motar cikin tsakiyar dare.
Hukumar ta KAROTA ta ce zata miƙa Giyar ga Hukumar Hizbah domin ɗaukar mataki na gaba da zarar ta kammala bincike.
Idan ba a manta ba Hukumar ta KAROTA ta miƙa Manyan motoci guda biyu wanda ta kama na giya ga Hukumar Hizbah da yawanta ya kai Kwalba dubu Arba’in da biyar (45,0000) wanda da kuɗinta ya haura naira miliyan Hamsin (50m).
A wani labarin kuma 👇👇👇
2023: Ya kamata INEC ta haramtawa Ƴan Takarar da ke ziyartar coci-coci da masallatai – Adeyanju