Jami’i dake kula da gudanar da rigafi a Jihar Neja Abubakar Usman Kpantu ya bayyana cewa an gudanar da rigafin Korona wa mutane kimanin dubu talatin da hudu da dari biyu da ashirin, yayin da allurar da ta rage ba ta wuce dubu talatin da takwas da dari tara da arba’in ba.
Abubakar Usman Kpantu ya bayyana haka ne yayin wani taron kara wa juna sani da cibiyar bunkasa harkokin bincike ta Jami’ar Tarayya dake Minna ta shirya wa yan jarida.
A cewar shi gwamnatin Jihar ta karbi allurar rigafin ne kimanin dubu saba’in da hudu da dari daya da goma inda ake sa ran za a yi mutane dubu sittin da biyar da dari biyu da ashirin da takwas, Kwatankwacin kashi daya cikin dari na al’ummar jihar.
Ya ce tun lokacin da aka fara gudanar da rigafin wa al’ummar jihar kawo yanzu, babu wani rahoton illar sa ya haifar ko da guda daya.
To sai dai ya ce Rigafin ya gamu da cikas bisa irin chamfi da aka yi Mishi na illa ga lafiyar al’umma, lamarin da ya kai ga har wasu jami’an lafiya ma na kaffa-kaffa wajen yin sa.
Daga bisani ya ja hankalin kafafwn yada labarai da su iya tasu wajen sun fadakar da jama’a kan muhimmancin rigafin.