Jami’an NCDSC na bukatar hadin kan Yan Najeriya domin inganta tsaro
Jami’an NCDSC reshen Jahar Akwa Ibom sunyi Kira ga Yan Najeriya dasu hada Kai da Jami’an tsaron kasar nan don tabbatar da tsaro.
Shugaban NCDSC na Jahar, Abidemi Majedenkunmi, ya bayyana haka ga manema labarai a birnin Oyo.
KARANTA:-Domin tsaro:- Hukumar FCTA ta rusa gini 400 da ba kan tsari ba, a Abuja
Abidemi yace “Jami’an tsaron zamani sukanyi amfani da bayani da suke samu domin yakar ta’addanci dake damun Kasa.
“Na da bukatar idan kaga abu ka sanar don cigaban Kasa da gina Al’umma.”
“Gwamnati ba za ta taba zama ba ba tare da hadin kan Al’umma ba.”
” Ya zama wajibin Al’umma da su hada Kai da gwamnati.”
“Ita dai gwamnati anyi ta ne domin Al’umma”
Kamar yadda yace, Hukumar NCDSC anyi sune don kare muhimman kayayyakin kasa
Kamar yadda ya ambata, hadin kan Yan kasa ya zama wajibi, sannan jami’an NCDSC zasu cigaba da tabbatar da tsaron Al’umma da kayayyakin kasa.
Ya kuma yi kira ga mazauna Jahar Akwa Ibom, da su zama mutane masu bin doka, sannan su rinka baiwa hukuma ingantattun labarai.
Comments 1